(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron majalisar koli ta al’adu da juyi, a jiya Talata, ya bayyana cewa; Yadda duniya za ta kasance bayan cutar corona da akwai banbanci matuka, kuma kuskure ne mu tsammaci cewa za a koma daidai cikin kankanen lokaci.
Shugaban kasar ta Iran ya yi ishara da cewa; A tsawon lokacin bullar cotar corona, duk wani taro da zama da za a yi sai an tuntubar kwamitin da ke fada da cutar ta corona, kuma wasu mahalarta taron kan yi ne ta hanyar video ba kai tsaye ba.
Dr. Hassan Rauhani ya yi wa sabon shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf barka da halartar taron majalisar wanda shi ne na farko a wurinsa bayan zabensa.
/129
18 Yuni 2020 - 08:30
Lambar labari: 1047733
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron majalisar koli ta al’adu da juyi, a jiya Talata, ya bayyana cewa; Yadda duniya za ta kasance bayan cutar